Posts

Showing posts from October, 2025

TUFAFIN MANZON ALLAH (S.A.W)

Image
Tufafin Annabi Muhammad (SAWW) Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallama ya kasance yana zaben mafi kyawun tufafi ba tare da girman kai, ko almubazzaranci ba. Zai zaɓi tufafin da ya fi dacewa da jikinsa, kuma ya sami motsawa cikin sauƙi (ba matsatstsun kaya ba, ba musu girman da ya wuce kima ba), ya na guje wa kaya masu fadi da yawa, ko musu dogon hannayen da suka wuce gabar hannu, da dogayen tufafin da suka wuce idon sawu. Rawaninsa bai yi girma da yawa ba kuma baiyi ƙanƙanta wajen kare zafi ko sanyi ba. Tufafinsa sun bambanta, wani lokaci yana sa na ulu wani lokaci na auduga. Yana sa tufafi daban-daban, kamar Alkyabba, Izar (ƙananan tufa), Burdah (alkyabba), Khameesah (shirt), da Mirt (rawani). A wasu lokuta, yakan sanya tufafin da aka keɓe kamar riguna da aka dinka, da Qubaa (tufafin da ake sanyawa akan riga). Bai yi riko da wani nau'in tufafi daya kawai ba. Bayanan sutturarsa sune kamar haka. Irin Tufafin Annabi Muhammad (SAWW) Isaba: Wannan yana nufin duk wani abu da ake nad...

LABARIN MAFARKIN MANZON ALLAH (S.A.W)

Image
Samurah bn Jundub (r.a) ya ce: Wata rana Manzon Allah (s.a.w) ya bamu labari, ya ce; Lallai jiya da dare wasu su biyu sun zo min, sai suka tashe ni, sannan suka ce da ni; mu tafi, sai na tafi tare da su. 1. Sai muka izo wani mutum a kwance, ga wani kuma a tsaye a kansa riƙe da 🪨 dutse, sai ya ɗauki wannan dutsen ya rotsa kan na kwancen har sai kansa ya fashe, dutsen ya yi gefe, idan ya tafi ɗauko dutsen kafin ya dawo, kan ya sake haɗewa, sannan ya sake rotsa masa dutsen a kansa! Sai na ce musu; Subhanallahi, su waye waɗannan kuma? Sai suka ce min; mu tafi, mu tafi, sai muka tafi. 2. Sai muka iso wani mutum yana kwance kan ƙeyarsa, ga wani kuma a tsaye a kansa riƙe da 🪝 ƙugiya na baƙin ƙarfe, sai ya zo gefen bakinsa ya sanya ƙugiyar nan, ya tsaga bakinsa har sai ƙugiyar ta fito ta ƙeyarsa, sannan ya sanya ƙugiyar a ƙofar hancinsa na gefe ɗaya, har sai ya huda ta fito ta ƙeyarsa, sannan ya saka ƙugiyar ta idonsa ɗaya, ya huda har sai ta fito ta ƙeyarsa, sannan ya cire ƙugiyar ya koma ɗ...

RANAR TA MANZON ALLAH (ﷺ) CE

Image
 Ranar da duk halitta zata taru Har Annabawa da Manzanni (As) kowa ta kansa yakeyi, Amma Annabin mu Muhammadu (ﷺ) shi kadai ne yake ta al'ummarsa, Ranar da Allah yayi fushin da bai taɓa yin irinsa ba, Kuma ba zai Qara yin irinsa ba, don haka dukkan Annabawa da Mala'iku babu wanda ya isa yin magana da Ubangiji ballantana ya nemawa kansa cheto ko al'ummarsa, Amma Annabi Muhammadu (ﷺ) shi kaɗai ne darajarsa ta kai yayi magana da Rabbul Izzati Wal Jalãli A wannan Ranar. Ranar da Jahannama za'a zo da'ita a hannun mala'iku dubu 70 tana fizga suna fizga tayi gunji tayi kururuwa tayi ma kanta kirari, duk wanda ke cikin wannan filin na Alqiyamah kowa sai ya durƙushe ƙasa akan gwiwarsa saboda tsananin tsoro, in banda Annabi Muhammadu (ﷺ). Ya RASULILLAHI kai zaka je kayi Sujjadah ga Rabbul Malakuti, kayi masa yabo da kirarin da babu wata halittar da ta taɓa yi masa Zai ce "YA MUHAMMADU YA MASOYINA! ƊAGO KANKA ROƘI (DUK ABINDA KAKE SO) ZA'A BAKA KUMA KA NEMI CHETO...

FALALAR RANAR JUMA’AH

Image
1-Ita ce mafi alkhairin ranaku a wajan Allah. Manzon Allah yace; (Mafi alkhairin ranaku a wajan Allah, itace ranar juma’a 2-Mafi alkhairin salloli a wajan Allah tana cikin ranar juma’a. Manzon Allah yace; (Mafi alkhairin salloli a wajan Allah, itace sallar assubar Ranar juma’a) 3-Manzon Allah yayi Umarni akan mu yawaita yin Salati a gareshi a Daren juma’a da yinin Juma’a. Manzon Allah yace; (Ku yawaita yin salati a gareni a Daren juma’a da yinin juma’a, dukkan wanda yayi min Salati guda daya,Allah zai yi masa Salati guda goma) 4-Wanda ya mutu ranar juma’a ko Daren juma’a, Allah yana bashi kariya daga fitinar Qabari. Manzon Allah yace; (Babu wani musulmi da zai mutu a ranar juma’a ko Daren juma’a, face sai Allah ya tseratar da shi daga fitinar Qabari 5-Samun kankarar zunubai daga juma’a zuwa wata juma’ar. Manzon Allah yace; (Salloli guda biyar na farilla,da juma’a zuwa wata juma’a, ana kankare zunuban da ke tsakaninsu idan an nisanci manyan laifuka) 6-Ana kankare zunuban da ya mutum yay...

ABUBUWA ASHIRIN (20) DA SUKE NUNA KANA SON MANZON ALLAH ﷺ

Image
Ga wasu abubuwa guda 20 da suke nuna cewa mutum yana son Manzon Allah ﷺ. Wannan soyayya ita ce ainihin alamar imani, domin Annabi ﷺ ya ce: بسم الله الرحمن الرحيم لَا يُؤْمِنُ أَحَدُكُمْ حَتَّى أَكُونَ أَحَبَّ إِلَيْهِ مِنْ وَالِدِهِ وَوَلَدِهِ وَالنَّاسِ أَجْمَعِينَ Fassara Annabi صلى الله عليه وسلم  Yace imanin dayanku bazai cika ba har sai yakasance nafi soyuwa a gareshi sama iyayensa da ya'yansa dama mutane gaba daya  1. Yarda da duk abin da ya zo da shi ﷺ  Wanda ya gaskata shi gaba ɗaya, bai yi musu da Alƙur’ani ko Hadisi ba. 2. Bin sunnarsa a rayuwa Koyi da yadda ya yi ibada, mu’amala, sallah, cin abinci, hulɗa da mutane. 3. Yawaita salati gare shi ﷺ Kamar yadda Allah Ya umurce mu: “Ku yi masa salati ku yi masa sallama. 4. Karanta tarihin rayuwarsa (Sīrah) Don sanin yadda ya rayu da yadda ya yi jihadi da da’awa. 5. Koyi da halayensa Gaskiya, amana, karamci, haƙuri, tausayi da kyautatawa. 6. Neman ilimi akan hadisan sa Domin koyon yadda ya yi ibada da koyarwa. 7. Guje...

SALLOLIN NAFILA KALA 8 DA YAKAMATA MU KIYAYE SU

Image
Kwadaitarwar da Manzon Allah SAW yayi na yawaita Sujada ga mai son makwabtaka da shi aaljanna, ya shafi yawaita sallar nafila ne ba sallar farilla ba, duk wanda yake son SALLOLIN farilla farilla nasa su kubuta a gobe alkiyama to ya yawaita sallar nafila.  Daga cikin Nafilolin da Manzon Allah SAW ya kwadaitar da mu mu kiyaye su sun hada da:- 1-NAFILOLI NA YAU DA KULLUM  Sune nafilolin da akeyi bayan sallolin farilla da wadanda ake kafin sallar farilla, addadinsu raka'a goma sha biyu ne kuma Dukkan su Manzon Allah SAW yana yin sune agida kamar yadda Hadisin Nana A'isha ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﺎ ta ruwaito @Saheehul Jami'i Daga Ummu Habibah ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﺎ tana cewa,Manzon Allah ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ yana cewa: (Wanda ya sallaci raka'a goma sha biyu acikin dare da yini na nafila, an gina masa gida acikin aljanna, Raka'a hudu kafin sallar Azzahar da biyu bayan ta, da raka'a biyu bayan magari ba da raka'a biyu bayan Isha'i da raka'a biyu kafin sallar Assuba bayan fitowar ...

KUSKUREN DA WASU MASU SALLAH KE YI TARE DA LIMAN

Image
 Na Farko. YAYAN LIMAN  Na Biyu. ABOKIN LIMAN  YAYAN LIMAN: Shine wanda yake yin aiki kafin liman yayi musamman; Farilla kamar ruku'u,sujada da sauransu. Wannan mutumin yana aikata kuskure kuma bai yi biyayya ga liman ba. Dalili shine manzon ALLAH  صلى الله عليه وسلم yace: إِنَّمَا جُعِلَ الإِمَامُ لِيُؤْتَمَّ بِهِ Ma'ana: An sanya liman domin ku yi koyi dashi; Idan yayi ruku'u kuma kuyi, idan yayi sujuda kuma kuyi. Dan haka yan uwa mu kiyaye! ABOKIN LIMAN: Shine wanda suke yin komai tare da liman idan liman zai yi ruku'u za suyi tare, ba zai jira liman yayi ba sannan shima yayi. Tabbas wannan ma kuskure ne ka da kayi komai a sallah sai liman ya gabatar. A takaice dai ba a yin wani aiki acikin sallah kafin liman kuma ba ayi a tare dashi dole sai yayi sannan mamu suyi wannan shine ladabi ga liman acikin Sallah. ALLAH Yasa mudace. Amin

SALLAR NAFILA LOKACIN HUDUBA A RANAR JUMA'AH

Image
1) Idan mutum ya shiga masallaci ranar Jumu'ah liman yana akan minbari, zaiyi sallah raka'ah biyu, amma ya gajarta. (Bukhari da Muslim) 2) Idan mutum ya taradda ana kiran sallah kafin a fara khutbah, zaiyi sallah lokacin da ake kira bazai jira a gama kiran sallah ba, saboda sauraron khutbah wajibi ne amma sauraron maikiran sallah Sunna ne. ( Ibn Uthaimeen) 3) Idan mutum bai samu shiga masallaci ba ya tsaya a harabar masallaci, bazaiyi sallah ba lokacin da liman ke khutbah, saboda sallar ta Tahiyyatul masjid ce, bata wajaba sai ga wanda ya shiga masallaci. 4) Mutane da yawa sukanyi kuskure sai su zata akwai wasu raka'ah biyu da akeyi kafin Jumu'ah, sai kaga mutum yazo yana wajen masallaci ya kabbarta sallah alhali liman yana khutbah. Wannan kuskure ne, matsayin sa kamar wanda ya tashi a cikin masallaci ya kabbarta sallah alhalin liman yana khutbah. 5) Duk wanda ya shiga masallaci wajibi ne (a kan zance mafi inganci) yayi sallah raka'ah biyu kafin ya zauna. Wannan huk...

SIRRIN SAMUN KWANCIN HANKALI: ABUBUWA GUDA HUƊU DA YA KAMATA KA DENA YI DAGA YAU

Image
Ya kai ɗan uwa, kwanciyar hankali kyauta ce mai daraja wadda dukiya ba za ta iya siya ba. Sau da yawa, mu da kanmu ne muke hana wa kanmu wannan kwanciyar hankalin ta hanyar wasu ɗabi'u da muke aikatawa. Idan kana son ka samu natsuwa ta gaskiya a rayuwarka, to ka yi alƙawarin za ka daina waɗannan abubuwa guda huɗu daga yau: 1. Ka Daina Damuwa da Abubuwan da Ba Za Ka Iya Canzawa Ba: A rayuwa, akwai abubuwan da suke ƙarƙashin ikonka, akwai kuma waɗanda ba za ka iya canza su ba. Damuwa a kan abin da ya wuce, ko kuma a kan yadda wasu mutane suke tunani a kanka, ɓata lokaci ne kawai. Ka mai da hankalinka kan abin da za ka iya canzawa—wato kanka, da ayyukanka, da kuma yadda kake kallon duniya. Abin da ya wuce ƙarfinka, ka bar wa Allah. 2. Ka Daina Kwatanta Rayuwarka da ta Wasu (Musamman a Social Media): Kwatanta kanka da wasu ita ce hanya mafi sauri ta sace wa kanka farin ciki. Ka tuna, a social media, kowa yana nuna maka ne babin da ya fi kyau a littafin rayuwarsa, amma ya ɓoye maka saur...

YADDA AKE YIN WANKAN HAILA DA JANABA

Image
 YADDA AKE WANKAN HAILA DA JANABA Zan gabatar da wannan ɗan taƙaitaccen rubutun ne a bisa dalilin yawa yawan tambayoyi da muke samu daga mata ƴan'uwanmu a game da yadda ake wankan haila ko wankan janaba.  WANKA shi ne game dukkan jiki da ruwa, kamar yadda ALLAH (ﷻ) Ya ce: “Idan kun kasance kuna da janaba kuyi tsarki.”  [suratul Ma'idah] WANKA farilla ce daga cikin farillolin da aka shar'antawa musulmi. WANKA suna da yawa amma WAJIBABBUN WANKA guda 4 ne: 1● Wankan ɗaukewar jinin haila. 2● Wankan ɗaukewar jini biƙi (haihuwa). 3● Wankan janaba. 4● Wankan shiga musulunci. A lura cewa dukkanin waɗannan wankan a aikace basu da banbamci shi ne wajen yin niyya, duk wanda za ayi daga ciki to za a gabatar da niyya akansa ne. WANKA yana da farillai guda biyar da sunnoni guda biyar da mustahabbi guda ɗaya kamar yadda mai littafin Ƙawa'idi ya faɗa, galibin mutane suna gabatar da shi gaba ɗaya domin neman lada, saboda haka ba sai na rarrabe su ba. WANKA Yana da siffofi guda biyu: SIF...

YADDA AKE YIN SALLAR WITR TARE DA KARATUN TA

Image
 🕌 Bayani game da yadda ake sallar Witr Lokaci: Ana yin sallar Witr ne bayan sallar Isha har zuwa kafin asuba (farkon sallar Fajr). 1️⃣ Adadin raka’o’i: Ana yin ta da raka’a 1, 3, 5, 7, ko fiye — amma mafi yawan mutane suna yin raka’a 3. 2️⃣ Idan raka’a uku ne: Hanya ta farko (madaidaiciya): Ka yi raka’a biyu ka yi sallama. Sannan ka yi raka’a ɗaya (1) daban. Wannan shi ne mafi inganci daga maganganun Annabi ﷺ. Hanya ta biyu (zai yi kama da Magrib): Ka yi raka’a uku kai tsaye, ba tare da sallama a tsakanin su ba, amma kar a karanta Tashahhud biyu — sai ɗaya a ƙarshe. 3️⃣ Abin da ake karantawa: Raka’a ta farko: Suratul Fātiha (الفاتحة) بِسْمِ اللّٰهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيمِ الْـحَمْدُ لِلّٰهِ رَبِّ الْعَالَمِينَ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيمِ مَالِكِ يَوْمِ الدِّينِ إِيَّاكَ نَعْبُدُ وَإِيَّاكَ نَسْتَعِينُ اهْدِنَا الصِّرَاطَ الْمُسْتَقِيمَ صِرَاطَ الَّذِينَ أَنْعَمْتَ عَلَيْهِمْ غَيْرِ الْمَغْضُوبِ عَلَيْهِمْ وَلَا الضَّالِّينَ Bismillāhir-raḥmānir-raḥīm. Al-ḥamdu lillāhi rabbil-‘ālamīn. A...

YADDA AKE YIN SALLAR TASBIH TARE DA KARATUN TA

Image
  Salātul Tasbīh (صلاة التسبيح) – wata nafila ce ta musamman da Annabi Muhammad ﷺ ya koya wa amminsa Abbas (RA), wadda take da lada mai girma idan aka yi ta yadda ya dace. Ga yadda ake Salatul Tasbih: 🌙 Adadin Raka’a: Raka’a 4 ne (ana yin su a raka’a ɗaya-ɗaya ko biyu-biyu). 🌿 Tsarin kowace raka’a: A cikin kowace raka’a ana karanta: Fātiha Sannan wata sura (misali Qul huwa Allāhu Aḥad ko Innā a‘ṭaināka al-kawthar) Bayan haka, ana karanta tasbih sau 15 kafin ruku’u: سُبْحَانَ اللَّهِ وَالْـحَمْدُ لِلَّهِ وَلَا إِلٰهَ إِلَّا اللَّهُ وَاللَّهُ أَكْبَرُ Subḥānallāhi wal-ḥamdu lillāhi wa lā ilāha illallāhu wallāhu akbar — (sau 15) 🔹 A yayin ruku’u: Bayan Subḥāna Rabbiyal ‘Aẓīm, sai a karanta wannan tasbih sau 10. سُبْحَانَ اللَّهِ وَالْـحَمْدُ لِلَّهِ وَلَا إِلٰهَ إِلَّا اللَّهُ وَاللَّهُ أَكْبَرُ Subḥānallāhi wal-ḥamdu lillāhi wa lā ilāha illallāhu wallāhu akbar — (sau 10) 🔹 Bayan daga ruku’u (Sami‘allāhu liman ḥamidah…): A karanta tasbih ɗin nan sau 10. 🔹 A cikin sujuda ta fark...

YADDA AKE YIN AZKAR

Image
Azkar” (أذكار) na nufin ambaton Allah (dhikr) — wato karatun addu’o’i da ambato bayan sallah, da safe, da yamma, da kuma kafin barci. Ga cikakken bayani yadda ake yin azkar: Ana karanta su bayan sallar Asuba har zuwa fitowar rana.  1. Ayatul Kursiyyu (Sau 1) Allāhu lā ilāha illā huwa al-ḥayyul-qayyūm, lā ta’khudhuhu sinatun walā nawm, lahu mā fī as-samāwāti wa mā fī al-arḍ, man dhalladhī yashfa‘u ‘indahu illā bi-idhnih, ya‘lamu mā bayna aydīhim wa mā khalfahum, walā yuḥīṭūna bishay’in min ‘ilmihī illā bimā shā’, wasi‘a kursiyyuhus-samāwāti wal-arḍ, walā ya’ūdūhu ḥifẓuhumā, wa huwa al-‘aliyyul-‘aẓīm. 2. Suratul Ikhlās (Sau 3) Qul huwa-llāhu aḥad Allāhuṣ-ṣamad Lam yalid wa lam yūlad Wa lam yakun lahu kufuwan aḥad 3. Suratul Falaq (Sau 3) Qul a‘ūdhu bi rabbil-falaq. Min sharri mā khalaq. Wa min sharri ghāsiqin idhā waqab. Wa min sharri an-naffāthāti fil-‘uqad. Wa min sharri ḥāsidin idhā ḥasad. 4. Suratun-Nās (Sau 3) Qul a‘ūdhu bi rabbin-nās. Malikin-nās. Ilāhin-nās. Min sharri al-wasw...

YADDA AKE YIN SALLAR FARILLA TARE DA KARATUN TA

Image
 Wannan bayani ne da yake dauke da yadda ake karatun sallah ko gyara karatun sallah. 1. Shiri kafin sallah (Niyya da Tsafta) Tsafta: Yi alwala (wuduʼ) bisa sharudda (nufin tsaftace jikinka daga najasa). Niyya: A zuciya ka yi niyyar yin sallah kaza saboda Allah. Misali: Na yi niyyar yin sallar Azahar raka’a huɗu farilla saboda Allah. (Ba a bayyane ba, a zuci kawai). 2. Farkon Sallah – Takbīratul Iḥrām ɗaga hannayen ka har kunne (maza) ko kafada (mata), ka ce: اللّٰهُ أَكْبَرُ Allāhu akbar 3. Duʻāʼul Iftitāḥ (Bayan Takbīra) > Ana karanta shi a raka’a ta farko kawai bayan takbīra: سُبْحَانَكَ اللَّهُمَّ وَبِحَمْدِكَ، وَتَبَارَكَ اسْمُكَ، وَتَعَالَى جَدُّكَ، وَلَا إِلٰهَ غَيْرُكَ Subḥānaka allāhumma wa biḥamdika, wa tabārakasmuka, wa taʻālā jadduka, wa lā ilāha ghayruka 4. Sūratu l-Fātiḥa > Ana karanta ta a kowane raka’a: بِسْمِ ٱللّٰهِ ٱلرَّحْمَـٰنِ ٱلرَّحِيمِ ٱلْـحَمْدُ لِلّٰهِ رَبِّ ٱلْعَـٰلَمِينَ ٱلرَّحْمَـٰنِ ٱلرَّحِيمِ مَـٰلِكِ يَوْمِ ٱلدِّينِ إِيَّاكَ نَعْبُدُ وَإِيَّاكَ ن...

YADDA AKE YIN TAIMAMA

Image
Tayammumi (taimama) ibada ce da ake yin ta idan ba a sami ruwa ba ko kuma ba a iya amfani da ruwa saboda wani uzuri (kamar rashin lafiya). Ga yadda ake yin tayammumi mataki-mataki: 1. Sharuddan Tayammumi Tayammumi yana halatta ne idan: Babu ruwa a kusa. Ruwa yana da nisa sosai. Ruwa yana da illa ga lafiya idan an yi amfani da shi. Ruwa yana da iyaka (misali ana buƙatarsa don sha). 2. Abin da ake amfani da shi Ƙasa mai tsabta (ko turɓaya, yashi, ƙasa mai laushi, ko dutse mai ƙura). > Lura: Ba a amfani da laka ko ƙasa da ruwa. 3. Ni'yya (Niyya) Kamar yadda ake yin niyya a wanka ko alwala, haka ma a tayammumi. > Misali: "Nawaitu tayammuma listibāḥatiṣ-ṣalāti lillāhi ta‘ālā" (Na yi niyyar yin tayammumi don yin salla saboda Allah Maɗaukaki.) 4. Yadda ake yin Tayammumi 1. Ka yi niyya a zuciya. 2. Ka Dora tafukan hannayen ka biyu a kan ƙasa (ko ƙura mai tsabta) sau ɗaya. 3. Ka share fuska da su gaba ɗaya. 4. Ka sake Dora tafukan hannayen ka biyu a ƙasa sau ɗaya, sannan: Ka...