RANAR TA MANZON ALLAH (ﷺ) CE

 Ranar da duk halitta zata taru Har Annabawa da Manzanni (As) kowa ta kansa yakeyi, Amma Annabin mu Muhammadu (ﷺ) shi kadai ne yake ta al'ummarsa, Ranar da Allah yayi fushin da bai taɓa yin irinsa ba, Kuma ba zai Qara yin irinsa ba, don haka dukkan Annabawa da Mala'iku babu wanda ya isa yin magana da Ubangiji ballantana ya nemawa kansa cheto ko al'ummarsa, Amma Annabi Muhammadu (ﷺ) shi kaɗai ne darajarsa ta kai yayi magana da Rabbul Izzati Wal Jalãli A wannan Ranar.

Ranar da Jahannama za'a zo da'ita a hannun mala'iku dubu 70 tana fizga suna fizga tayi gunji tayi kururuwa tayi ma kanta kirari, duk wanda ke cikin wannan filin na Alqiyamah kowa sai ya durƙushe ƙasa akan gwiwarsa saboda tsananin tsoro, in banda Annabi Muhammadu (ﷺ).

Ya RASULILLAHI kai zaka je kayi Sujjadah ga Rabbul Malakuti, kayi masa yabo da kirarin da babu wata halittar da ta taɓa yi masa Zai ce "YA MUHAMMADU YA MASOYINA! ƊAGO KANKA ROƘI (DUK ABINDA KAKE SO) ZA'A BAKA KUMA KA NEMI CHETO A BAKA!!.

Babu wanda ya kai wannan Matsayin sai dai Kai..

Assalamu alaika Ayyuhan~Nabiyyu wa

Rahmatullahi wa barakatuhu.

Assalamu alaika Ayyuhash Shafi'ul Mushaffa'i.

Assalamu alaika Yã Sãhibul Maqamil Mahmud.

ALLAH YASAMU CIKIN CETONSA

ALBAKACIN ANNABI MUHAMMADU SAWW AMEN YARABBI.



Comments

Popular posts from this blog

YADDA AKE YIN WANKAN HAILA DA JANABA

YADDA AKE YIN AZKAR