SALLOLIN NAFILA KALA 8 DA YAKAMATA MU KIYAYE SU
Kwadaitarwar da Manzon Allah SAW yayi na yawaita Sujada ga mai son makwabtaka da shi aaljanna, ya shafi yawaita sallar nafila ne ba sallar farilla ba, duk wanda yake son SALLOLIN farilla farilla nasa su kubuta a gobe alkiyama to ya yawaita sallar nafila.
Daga cikin Nafilolin da Manzon Allah SAW ya kwadaitar da mu mu kiyaye su sun hada da:-
1-NAFILOLI NA YAU DA KULLUM
Sune nafilolin da akeyi bayan sallolin farilla da wadanda ake kafin sallar farilla, addadinsu raka'a goma sha biyu ne
kuma Dukkan su Manzon Allah SAW yana yin sune agida kamar yadda Hadisin Nana A'isha ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﺎ ta ruwaito
@Saheehul Jami'i
Daga Ummu Habibah ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﺎ tana cewa,Manzon Allah ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ yana cewa:
(Wanda ya sallaci raka'a goma sha biyu acikin dare da yini na nafila, an gina masa gida acikin aljanna, Raka'a hudu kafin sallar Azzahar da biyu bayan ta, da raka'a biyu bayan magari ba da raka'a biyu bayan Isha'i da raka'a biyu kafin sallar Assuba bayan fitowar alfijir)
@ﺭﻭﺍﻩ ﺍﻟﺘﺮﻣﺬﻱ ( 415 )
®Raka'a 4 kafin Azzahar
®Raka'a 2 bayan Azzahar
®Raka'a biyu bayan Magariba
®Raka'a biyu bayan Isha'i
®Raka'a biyu kafin sallar assuba
Tambihi
Dukkan wadan nan nafilfili ana so ayi su a gida ne idan da iko, idan kuma babu sai ayi su a duk inda ya saukaka.
2-RAKA'A BIYU BAYAN FITOWAR ALFIJIR KAFIN SALLAR ASSUBA
Wannan itace sunnar Alfijir wato idan anyi kiran salla na biyu bayan fitowar alfijir kafin sallar Assuba za'a nafula raka'a biyu kuma ayi su a sayukake.
Manzon Allah ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ya kasance yana kiyaye raka'a biyu kafin sallar assuba a kowace rana, kuma yana yin su koda yana lokacin tafiyane.
Manzon Allah ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ yana cewa:
(Yin sallar nafila raka'a biyu bayan fitowar alfijir yafi duniya da abinda yake cikin ta alkhairi).
@ﺭﻭﺍﻩ ﻣﺴﻠﻢ ( 725 )
3-RAKA'A HUDU KAFIN SALLAR AZZAHAR,DA HUDU BAYAN AZZAHAR
Manzon Allah SAW ya kwadaitar akan yin raka'a hydu kafin sallar Azzahar na nafila kuma idan suka kubucewa mutum yana da damar ramasu a bayan sallar Azzahar.
Nana A'isha ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﺎ tana cewa,Manzon Allah ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ya kasance idan baiyi raka'a hudu ba na nafila kafin sallar Azzahar to yana ramasu bayan sallar Azzahar.
@ﺭﻭﺍﻩ ﺍﻟﺘﺮﻣﺬﻱ ( 426 )
Manzon Allah SAW yana cewa
(Wanda ya kiyaye raka'a hudu kafin sallar Azzahar da hudu bayanta, to Allah ya haramtawa wuta cin namansa)
@ﺭﻭﺍﻩ ﺍﻟﺘﺮﻣﺬﻱ ( 428 ) ﻭﺻﺤﺤﻪ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ ( 6195 )
4-SALLAR WALLAHA
Itace sallar nafilar da ake yinta bayan rana ta fito ta dago kadan kuma ake daina yinta bayan rana ta karkata daga tsakiya, lokacin da akafi so ayita shine Lokacin da rana tayi zafi sosai wato kamar karfe 11:00 zuwa 1l11:45am.
Sallar Wallaha raka'a guda biyu daidai yake da yin sadaka 360 na gabban dan Adam.
Manzon Allah SAW yana cewa:
(Dukkan jikin dan adam yana wayuwar gari a dorawa kowace gaba ta jikinsa aikin Sadaka, kuce Alhamdulillahi sadakace, kowace Laa ilaha illah sadakce, kawace Allahu akbar sadakace,.......... Yin sallar wallaha raka'a biyu ta isar ga wannan ga wannan sadaka gaba daya)
@ﺭﻭﺍﻩ ﻣﺴﻠﻢ ( 720 )
Manzon Allah SAW yana cewa;
(Lallai Allah mai girma da daukaka yana cewa;"Ya kai dan Adam,ka kiyayemin salloli raka'a hudu a farkon yini,zan kiyaye maka zuwa karshen yinika)
@ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺘﺮﻏﻴﺐ 671 ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ
5-YIN NAFILA RAKA'A HUDU KAFIN SALLAR LA'ASAR
Sunnar Manzon Allah SAW ce mustahabbiya yin sallar nafila raka'a hudu kafin sallar La'asar bayan ankira sallar Laa'asar, amma bata ciki sunnoni RATIBAI NA YAU DA KULLUM, sai dai Manzon Allah SAW ya kwadaitar da yinsu tare da addu'a ta musamman ga wanda ya aikata ta.
Manzon Allah SAW yana cewa:
(Allah kayi rahama da jin kai ga wanda yayi sallar nafila raka'a hudu kafin sallar La'asar).
@ﺭﻭﺍﻩ ﺍﻟﺘﺮﻣﺬﻱ ( 430 ) ﻭﺃﺑﻮ ﺩﺍﻭﺩ ( 1271 )
6-SALLAR HANTSI
Wato ita ce sallar da mutum yake yinta bayan rana ta fito ba jimawa, amma da sharadin yana zaune tun daga sallar assuba a inda yakd yana azkar har rana ta fito sai ya tashi yayi sallar nafila raka'a biyu, yin wannan sallah yana da lada mai yawa
Manzon Allah SAW yana cewa:
(Wanda yayi sallar Assuba acikin jam'i sannan ya zauna yana ta ambaton Allah har rana ta fito, sannan yayi sallah raka'a biyu, yana da lada kamar ladar hajji da Umara cikakku cikakku)
@ﺭﻭﺍﻩ ﺍﻟﺘﺮﻣﺬﻱ .
7-SALLAR NAFI A CIKIN DARE
Manzon Allah SAW baya barin yin sallar nafilar dare alokacin rayuwarsa,shiya sanya malamai suka ce, yin sallar nafila ta dare akan Annabi SAW wajibine, amma akan sauran al'ummarsa sunnace mai karfi.
Manzon Allah SAW ya kasance ko baya da lafiyane yana yin sallar nafilar dare a zaune, kuma yana kara dagewa da wannan sallar a dararen goman karshe na watan Ramadhana.
Annabi SAW yace:
(Mafi alkhairi da falalar Sallah bayan sallar Farillah,itace Sallar lafiyar cikin Dare).
@ﺭﻭﺍﻩ ﻣﺴﻠﻢ ( 1163.
Manzon Allah SAW yace:
(Inayi maku wasiyya akan kuyi riko da Sallar cikin dare,domin Dhabi’ar mutanan kirkice ta wadanda suka zo kafinku,Kuma tana kusantar da ku zuwq ga Ubangijinku,kuma kankarar zunubaice agareku,kuma tana goge laifuka).
@ﺣﺴﻨﻪ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ ﻓﻲ ﺇﺭﻭﺍﺀ ﺍﻟﻐﻠﻴﻞ ( 452 )
Annabi SAW yana cewa:
(Lallai acikin aljanna akwai wani katafaren Bene,ana ganin cikinsa daga waje, kuma ana ganin wajansa daga cikinsa,) sai wani.
Balaraban Kauye yace:
“Na wanene ya Manzon Allah??” Sai yace:
(Na wanda yake:
-Kyautata magana
-Yake ciyar da abinci dan Allah
-Kuma yake azumin Nafila
-kuma ya tashi yake sallar dare lokacin da mutane suke barci).
@ﺣﺴﻨﻪ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ ﻓﻲ ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺘﺮﻣﺬﻱ
Manzon Allah ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ yana cewa:
(Idan dayanku namiji ya tayar da matarsa acikin dare, sai sukayi sallah tare ko sukayi sallah raka'a biyu, za'a rubuta su cikin masu ambaton Allah mai yawa Maza da mata)
@ﺭﻭﺍﻩ ﺃَﺑُﻮ ﺩﺍﻭﺩ ( 1451 )
8-SALLAR WUTIRI
Sallar wutiri tana da Falala da matsayi mai girma, babban abin da yake nuni akan falalarta da matsayin ta shine:
"Manzon Allah ﷺ bai taba barin yin sallar wutiri ba, a lokacin yana gida ko lokacin tafiya har ya koma zuwa ga ubangijinsa".
Daga Abi Basrata رضي الله عنه, Yace lallai Manzon Allah ﷺ yace:
(Lallai Allah yayi maku karin kyautar wata salla, to ku sallace ta a tsakanin sallar Isha'i zuwa sallar Assuba).
@رواه أحمد.
Manzon Allah SAW ya kasance yana yin wasiyya da yin sallar wutiri, wutiri sunnace mai karfi koda da raka'a dayane yayi. abinda ake nufi da wutiri shine mara wanda baya da hadi wato 1 ko 3 ko 5 da dai sauran su, ita sallar wutiri itace sallar da mutum yake mara wadda yake rufe nafilar dare da ita
Allah ne Mafi sani.
Allah ya bamu ikon aikatawa.

Comments
Post a Comment
Rubuta Mana Sharhin Ku Game Da Wannan.