LABARIN MAFARKIN MANZON ALLAH (S.A.W)

Samurah bn Jundub (r.a) ya ce: Wata rana Manzon Allah (s.a.w) ya bamu labari, ya ce;

Lallai jiya da dare wasu su biyu sun zo min, sai suka tashe ni, sannan suka ce da ni; mu tafi, sai na tafi tare da su.

1. Sai muka izo wani mutum a kwance, ga wani kuma a tsaye a kansa riƙe da 🪨 dutse, sai ya ɗauki wannan dutsen ya rotsa kan na kwancen har sai kansa ya fashe, dutsen ya yi gefe, idan ya tafi ɗauko dutsen kafin ya dawo, kan ya sake haɗewa, sannan ya sake rotsa masa dutsen a kansa!

Sai na ce musu; Subhanallahi, su waye waɗannan kuma? Sai suka ce min; mu tafi, mu tafi, sai muka tafi.

2. Sai muka iso wani mutum yana kwance kan ƙeyarsa, ga wani kuma a tsaye a kansa riƙe da 🪝 ƙugiya na baƙin ƙarfe, sai ya zo gefen bakinsa ya sanya ƙugiyar nan, ya tsaga bakinsa har sai ƙugiyar ta fito ta ƙeyarsa, sannan ya sanya ƙugiyar a ƙofar hancinsa na gefe ɗaya, har sai ya huda ta fito ta ƙeyarsa, sannan ya saka ƙugiyar ta idonsa ɗaya, ya huda har sai ta fito ta ƙeyarsa, sannan ya cire ƙugiyar ya koma ɗayan gefen shi ma ya masa haka, kafin ya gama da ɗayan gefen, gefen farko ya dawo yadda ya ke, sannan ya sake dawowa gareshi.

Sai na ce musu; Subhanallahi, su waye waɗannan kuma? Sai suka ce min; mu tafi, mu tafi, sai muka tafi.

3. Sai muka iso wani 🕳️ rami kamar kasko, samansa a tsuke, ƙasansa kuma da faɗi, ga ihu da kururuwa na fitowa daga ciki, sai muka leƙa ciki sai ga maza da mata tsirara, ana hura 🔥 wuta ta ƙasansu, idan aka huro wutar, sai ta ɗaga su sama sai su fara ihu suna kuka, sai sun yi kamar za su fito, sai a kashe ta sai su koma ciki, sannan a sake huro ta.

Sai na ce musu; su waye waɗannan kuma? Sai suka ce min; mu tafi, mu tafi, sai muka tafi.

4. Sai muka iso wata 🌊 ƙorama ta jini, sai ga wani mutum a cikin wannan ƙoramar yana 🏊‍♀ iyo, ga wani kuma a gaɓar ƙoramar ya tara duwatsu a gabansa. Idan na cikin jinin nan ya so fitowa, sai ya jefe shi da dutse har cikin bakinsa, sai jifan nan ya mai da shi cikin jinin ya ci gaba da iyo, duk sanda ya yi yunƙurin fitowa sai na gaɓar ƙoramar ya jefe shi da dutse ya mai da shi.

Sai na ce musu; su waye waɗannan kuma? Sai suka ce min; mu tafi, mu tafi, sai muka tafi.

5. Sai muka iso wajen wani 👺 mummunan mutum, mafi munin mutum da ka taɓa gani, a gefensa akwai 🔥 wuta yana hura ta, yana gewaye ta. 

Sai na ce musu; waye wannan kuma? Sai suka ce min; mu tafi, mu tafi, sai muka tafi. 

6. Sai muka iso wani 🏕️ dausayi kore, cikinsa akwai dukkan nau'i na idaniyar ruwa, a tsakiyan dausayin nan sai ga wani mutum mai tsayi har kusan ba na iya ganin kansa saboda tsayi, a gewaye da mutumin nan kuwa akwai yara ƙanana da ban taɓa ganin masu yawansu ba.

Sai nace musu; waye wannan kuma? Kuma su waye waɗannan yaran? Sai suka ce min; mu tafi, mu tafi, sai muka tafi. 

7. Sai muka iso wajen wata ƙatuwar 🌳 bishiya, ban taɓa ganin bishiya mai girmanta ko kyanta ba, sai suka ce da ni hau, sai muka hau, sai muka iso wani birni da aka gina shi da 🧱 bulo na zinare da azurfa, sai muka je 🚪ƙofar birnin, muka ƙwanƙwasa, aka buɗe mana, sai muka shiga ciki, sai muka ga wasu mazaje rabin jikinsu kyakkyawa, mafi kyawun abinda ka taɓa gani, rabin jikinsu kuma mafi munin abinda ka taɓa gani. Sai suka ce musu ku je ku shiga waccar ƙoramar, sai ga wata ƙorama tana gudana, ruwan cikin kai kace madara ne saboda farinsa! Sai suka je suka faɗa ciki, sannan suka dawo garemu, sai ga gefensu mummunan nan ya tafi, sun dawo kyawawa gaba ɗaya.

Sai suka ce min wannan ita ce Aljannar zama (Jannãtu Adn), wancan kuma shi ne gidanka, ɗaga kanka sama, sai na ɗaga kai na sama, sai ga wani gida can sama fari kamar 🌫️ gajimare.

Sai na ce musu Allah Ya muku albarka, ku bar ni na shiga ciki, sai suka ce ai da sauran shekarun da suka rage maka (a duniya) da ka gama cika su da ka shiga, amma za ka shiga.

Sai nace musu lallai a daren nan na ga abubuwan al'ajabi da yawa, meye waɗannan abubuwan da na gani?.

Sai suka ce min lallai za mu baka labarin abubuwan da ka gani;

1. Amma ka ga mutum na farko da ka ga ana fasa kansa da dutse, to shi ne wanda Allah Ya bawa Alkur'ani amma ba ya karanta shi, ba ya aiki da shi.

2. Amma ka ga mutumin da ka wuce ana huda bakinsa da hancinsa da idonsa. To shi ne wanda ke yaɗa ƙaryar da ke yawo lungu da saƙo.

3. Amma ka ga maza da mata da suke tsirara ake toya su a cikin rami. To waɗannan mazinata kenan.

4. Amma ka ga mutumin da ka ga yake iyo a cikin ruwan jini ana jifansa da dutse. To wannan maciyin riba kenan.

5. Amma ka ga mummunan mutumin nan da ka gani wanda ke hura wuta yana gewaye ta, to wannan Mãliku kenan, mai tsaron wuta.

6. Amma ka ga mutum mai tsayin nan da ka gani a cikin wannan dausayin, to Ibrahim (a.s) kenan. Amma su kuma yaran da ka gani a gewaye da shi, to yaran mutane da suka mutu suna ƙanana kenan.

7. Amma ka ga mutanen da ka ga rabin jikinsu mai kyau, rabin kuma mummuna. To su ne waɗanda (a duniya) suka cakuɗa ayyuka, rabin aikinsu kyakkyawa rabinsa mummuna. Sai Allah Ya musu afuwa. Ni kuma ni ne Jibrilu, wannan kuma Mika'ilu ne.

📚 بخاري، كتاب التعبير، باب تعبير الرؤيا بعد صلاة الصبح( 7047)

📚 مسلم، كتاب الرؤيا، باب رؤيا النبي صلى الله عليه وسلم( 2275)



Comments

Popular posts from this blog

YADDA AKE YIN WANKAN HAILA DA JANABA

YADDA AKE YIN AZKAR