YADDA AKE YIN WANKAN HAILA DA JANABA
YADDA AKE WANKAN HAILA DA JANABA
Zan gabatar da wannan ɗan taƙaitaccen rubutun ne a bisa dalilin yawa yawan tambayoyi da muke samu daga mata ƴan'uwanmu a game da yadda ake wankan haila ko wankan janaba.
WANKA shi ne game dukkan jiki da ruwa, kamar yadda ALLAH (ﷻ) Ya ce: “Idan kun kasance kuna da janaba kuyi tsarki.” [suratul Ma'idah]
WANKA farilla ce daga cikin farillolin da aka shar'antawa musulmi.
WANKA suna da yawa amma WAJIBABBUN WANKA guda 4 ne:
1● Wankan ɗaukewar jinin haila.
2● Wankan ɗaukewar jini biƙi (haihuwa).
3● Wankan janaba.
4● Wankan shiga musulunci.
A lura cewa dukkanin waɗannan wankan a aikace basu da banbamci shi ne wajen yin niyya, duk wanda za ayi daga ciki to za a gabatar da niyya akansa ne.
WANKA yana da farillai guda biyar da sunnoni guda biyar da mustahabbi guda ɗaya kamar yadda mai littafin Ƙawa'idi ya faɗa, galibin mutane suna gabatar da shi gaba ɗaya domin neman lada, saboda haka ba sai na rarrabe su ba.
WANKA Yana da siffofi guda biyu: SIFFATUL KAMAL (wanka ta kamala) da SIFFATUL IJZA (wanka wacce ta wadatar)
1● SIFFATUL KAMAL ita ce wankan da ake binta a aikace lungu da saƙo wacce ita ce tafi lada fiye da ta biyun.
2● SIFFATUL IJZA ita ce wankan da mutum zai iya yin niyya ya faɗa cikin ƙududdufi ko swimmingf pool ya halatta kamar yadda yazo a cikin Sahihul Muslim, sai dai wanda yayi wanka irin na farkon yafi kamala saboda yabi dukkan sharuɗa.
YADDA AKE WANKA: Ana farawa ne da ɗaura niyya, za a yi niyyar wankan da za a yi na haila ko na janaba tare da ƙudurcewa a zuciya ba akan harshe ba, domin zuciya ita ce muhallin yin niyya. Za a wanke hannaye zuwa wuyan hannu sau uku. Za a wanke duk wani datti na daga jini ko maniyi daga cibiya zuwa cinyoyi ko zuwa guiwa. Za a wanke guraben alwala sau ɗaɗɗaya (wanki ɗaya) alwala irin wacce ake yi na sallah. Za a zubawa kai ruwa sau uku ta yadda ruwan zai kai ga cikin kayin sosai. Za a fara kwara ruwa a gefen jiki na dama tare da cuccuɗawa. Sai a kwara ruwa a gefen jiki na hagu tare da cuccuɗawa. Ya halatta a wanke ƙafafu tare da alwala idan anso kuma sai a jinƙirta sai an kammala wanka, duka biyun babu laifi domin sun tabbata daga Manzon ALLAH (ﷺ).
Wannan shi ne WANKA a taƙaice, abin da na faɗa dai-dai ALLAH ya haɗamu a ladar baki ɗaya , abin da na fada bisa kuskure ALLAH Ya gafarta min (Aameen).










Comments
Post a Comment
Rubuta Mana Sharhin Ku Game Da Wannan.