KUSKUREN DA WASU MASU SALLAH KE YI TARE DA LIMAN
Na Farko. YAYAN LIMAN
Na Biyu. ABOKIN LIMAN
YAYAN LIMAN: Shine wanda yake yin aiki kafin liman yayi musamman; Farilla kamar ruku'u,sujada da sauransu. Wannan mutumin yana aikata kuskure kuma bai yi biyayya ga liman ba. Dalili shine manzon ALLAH
صلى الله عليه وسلم yace: إِنَّمَا جُعِلَ الإِمَامُ لِيُؤْتَمَّ بِهِ
Ma'ana: An sanya liman domin ku yi koyi dashi; Idan yayi ruku'u kuma kuyi, idan yayi sujuda kuma kuyi.
Dan haka yan uwa mu kiyaye!
ABOKIN LIMAN: Shine wanda suke yin komai tare da liman idan liman zai yi ruku'u za suyi tare, ba zai jira liman yayi ba sannan shima yayi. Tabbas wannan ma kuskure ne ka da kayi komai a sallah sai liman ya gabatar.
A takaice dai ba a yin wani aiki acikin sallah kafin liman kuma ba ayi a tare dashi dole sai yayi sannan mamu suyi wannan shine ladabi ga liman acikin Sallah.
ALLAH Yasa mudace. Amin

Comments
Post a Comment
Rubuta Mana Sharhin Ku Game Da Wannan.