FALALAR RANAR JUMA’AH
1-Ita ce mafi alkhairin ranaku a wajan Allah.
Manzon Allah yace;
(Mafi alkhairin ranaku a wajan Allah, itace ranar juma’a
2-Mafi alkhairin salloli a wajan Allah tana cikin ranar juma’a.
Manzon Allah yace;
(Mafi alkhairin salloli a wajan Allah, itace sallar assubar Ranar juma’a)
3-Manzon Allah yayi Umarni akan mu yawaita yin Salati a gareshi a Daren juma’a da yinin Juma’a.
Manzon Allah yace;
(Ku yawaita yin salati a gareni a Daren juma’a da yinin juma’a, dukkan wanda yayi min Salati guda daya,Allah zai yi masa Salati guda goma)
4-Wanda ya mutu ranar juma’a ko Daren juma’a, Allah yana bashi kariya daga fitinar Qabari.
Manzon Allah yace;
(Babu wani musulmi da zai mutu a ranar juma’a ko Daren juma’a, face sai Allah ya tseratar da shi daga fitinar Qabari
5-Samun kankarar zunubai daga juma’a zuwa wata juma’ar.
Manzon Allah yace;
(Salloli guda biyar na farilla,da juma’a zuwa wata juma’a, ana kankare zunuban da ke tsakaninsu idan an nisanci manyan laifuka)
6-Ana kankare zunuban da ya mutum yayi na kwana goma a ranar juma’a.
Manzon Allah yace;
(Daga juma’a zuwa wata juma’a ana kankare zunuban dake tsakanin su idan an nisanci alfasha)
7-Yin wankan zuwa juma’a.
Manzon Allah yace;
(Idan dayan ku zaije zuwa juma’a to yayi Wankan juma’a)
8-Karanta Suratul Kahfi.
Manzon Allah yace;
(Wanda ya karanta suratul Kahfi ranar juma’a,Allah zai sanya masa wani haske zuwa wata juma,a.
ya Allah kadatar damu Alkhairin dake cikin wannan Rana Mai tarin Albarka Ameen 🤲

Comments
Post a Comment
Rubuta Mana Sharhin Ku Game Da Wannan.