YADDA AKE YIN WANKAN HAILA DA JANABA
YADDA AKE WANKAN HAILA DA JANABA Zan gabatar da wannan ɗan taƙaitaccen rubutun ne a bisa dalilin yawa yawan tambayoyi da muke samu daga mata ƴan'uwanmu a game da yadda ake wankan haila ko wankan janaba. WANKA shi ne game dukkan jiki da ruwa, kamar yadda ALLAH (ﷻ) Ya ce: “Idan kun kasance kuna da janaba kuyi tsarki.” [suratul Ma'idah] WANKA farilla ce daga cikin farillolin da aka shar'antawa musulmi. WANKA suna da yawa amma WAJIBABBUN WANKA guda 4 ne: 1● Wankan ɗaukewar jinin haila. 2● Wankan ɗaukewar jini biƙi (haihuwa). 3● Wankan janaba. 4● Wankan shiga musulunci. A lura cewa dukkanin waɗannan wankan a aikace basu da banbamci shi ne wajen yin niyya, duk wanda za ayi daga ciki to za a gabatar da niyya akansa ne. WANKA yana da farillai guda biyar da sunnoni guda biyar da mustahabbi guda ɗaya kamar yadda mai littafin Ƙawa'idi ya faɗa, galibin mutane suna gabatar da shi gaba ɗaya domin neman lada, saboda haka ba sai na rarrabe su ba. WANKA Yana da siffofi guda biyu: SIF...
Comments
Post a Comment
Rubuta Mana Sharhin Ku Game Da Wannan.